Fitaccen jarumin nan masana’atar Kannywood Lawal ahmed wanda yake da suna a cikin shiri mai dogon zango da ya samu karbuwa Izzah so umar hashim.
Ya kawo wasu sharuda wanda duk yake son ya daina shiri mai dogon zango na izzah so, wasu na ganin wannan zance sam bai dace ya fito daga bakinsa, idan bazaku manta ba a kwanakin baya yayi irin wannan zance inda yake cewa duk wanda yake tambayar yaushe za’a gama shirin izzar so to baya kishin musulunci.
To shine yau ma jarumi yazo da wasu sharuda da ya wallafa sa shafinsa na sada zumunta facebook mai suna @lawanahmad yana mai cewa
kuje kusa a daina cin kasuwar kwari,da singa,da kasuwar rimi , da sabon gari kusa a rufe duk wani gidan mai da yake shayarda mai.
Kusa a dena zuwa makaranta ,kusa a rufe gidan gwamnati,ku sa a dena zuwa kowace kasuwa da duk sauran duk wani gari da ake yin kasuwanci.
Saboda haka anayine don kasuwanci nima inayin izzar so ne don kasuwanci.
Nagode”.– inji lawal Ahmad.