DANDALIN TWITTER
Ba aure ne bana so ba kaje kana tuɓe kaya a gaban wani ƙaton Namiji nida nake da kunya—Mariya
Kamar yadda kuka sani shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media sun yi fice waje jawo ce-ce-kuce da muhawara a tsakanin mabiya inda ƴan mata da samari da dama suke baje kolinsu.
Wasunsu na amfani da waɗannan kafafe wajen gudanar da harakokin kasuwanci yayin da wasu ke yin barkwanci kuma kamar yadda kuka sani ne wasu suna neman abokan rayuwa.
Ta yadda zaku ga wasu ƴan mata da samarin suna neman mazajen aure wasun su dagaske suke yayin da wasu kuma don ayi raha kawai suke yin rubuce-rubuce a shafukan nasu
Wata matashiya mai suma Mariya ta bayya a shafinta na Twitter cewa “Ba Aure bane banaso kaje kana tube Kaya a gaban wani Katowice Namiji ni da nake da Kunya”